Post Top Ad

Post Top Ad

Tuesday, October 2, 2018

October 02, 2018

NEWS: Labari cikin hotuna Tsohon gwamnan Katsina ya raka diyar shi dakin auren ta

Ibrahim Shema ya raka diyar shi har dakin aure ta bayan ya daura mata aure ga Huzaifa.



Ba saban ba, tsohon gwamnan jihar Katsina, Ibrahim Shema, ya raka babban diyar shi zuwa dakin aurenta bayan ya daura mata aure.


Bayar yadda al'adda ta tanadar, bayan shagulgulan bikin aure, iyaye sukan raka amarya zuwa dakin mijin ta. Mafi yawanci iyaye mata ke raka amarya dakin aure sai dai tsohon gwamnan bai gaza nuna kaunar dake tsakanin sa da diyar shi inda ya raka ta tare da rike hannun ta har zuwa dakin ta.














Kamar yadda za'a gani cikin kayatattun hotuna da aka fitar na bikin an gan inda amaryar take kukan rabuwa da iyalen ta.

Aisha Ibrahim Shema ta amarce ga angon ta Huzaifa a makon da shude kana anyi shagalin bikin auren su a garin Abuja.
October 02, 2018

POLITICS: Atiku Abubakar Buhari ya raba kawunan yan Nijeriya - inji tsohon mataimakin shugaban kasa



Ya ayyana hakan ne yayin da jirgin yakin neman zaben sa ta sauka jihar Anambra ranar Laraba 26 ga watan Satumba.






    Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, wanda ke neman haye kujerar shugaban kasa ya sake caccakar gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari.

    Yace gwamnatin shugaban ta raba kawunan yan Nijeriya.

    Ya ayyana hakan ne yayin da jirgin yakin neman zaben sa ta sauka jihar Anambra ranar Laraba 26 ga watan Satumba.

    Kamar yadda Daily post ta ruwaito, dan takarar yace an samu wannan abun bakin ciki a kasar domin yan Nijeriya sun zabi wanda bai cancanta ba.

    Da yake jawabi a taron da yayi da magoya bayan jam'iyar PDP na jihar Anambra, Atiku yace akwai bukatar gwamnati da sauya fasalin kasa kana ta yarda ko wacce yankin ta gudanar da alamuran shugabanci da kanta.



    Ya cigaba da sukar gwamnatin APC ta yanzu inda ya bada misalin bangarorin da ta gaza samun cigaba da zai tallafa ma rayuwar yan kasa.

    Ya bada misali a bangaren kiwon lafiya, harkar kasuwanci, aikin yi da kuma ayyukan walwala.

    Tsohon mataimakin shugaba Obasanjo yayi kira ga yan jam'iyar PDP na jihar da su goyi bayan takarar sa na zama gwanin PDP gabanin zaben 2019.

    Yayi ma al'ummar yankin kudu maso gabas alkawarin gina filin sauka da tashin jirgin sama na kasashe-da-kashe idan yayi nasarar zama shugaban kasa a zaben 2019.

    Atiku yana daya daga cikin yan takara 15 dake neman lashe zaben fidda gwani na jam'iyar PDP domin fafata da yan takarar sauran jam'iyu a zaben gobe.

    October 02, 2018

    POLITICS: Rabiu Musa Kwankwaso Zan doke Buhari cikin ruwan sanyi a zaben 2019

    Dan majalisar dattawan yayi wannan ikirari ne yayin da jirgin neman zaben sa ya kai ziyarar jihar filato ranar alhamis 27 ga watan satumba.





    Tsohon gwamnan jihar Kano kuma daga daga cikin yan takarar shugaban kasa na jam'iyar PDP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, yace zai doke shugaba Buhari cikin ruwan sanyi idan ya zama dan takarar jam'iyar sa a zaben 2019.

    Dan majalisar dattawan yayi wannan ikirari ne yayin da jirgin neman zaben sa ya kai ziyarar jihar filato ranar alhamis 27 ga watan satumba.

    Jagoran tafiyar Kwankwasiya yace yana da darajan kwato tutar mulki daga hannun jam'iyar APC a zaben gobe.


    Yana mai cewa "idan na zama gwanin PDP , ni zan zama shugaban Nijeriya".

    Kwankwaso yayi ikirari cewa yana da dinbim magoya a yankin arewa yamma kuma yawan su zai karu muddin jam'iyar PDP ta bashi damar zama dan takarar ta.

    Ya kuma soki gwamnati mai mulki ta APC inda yace ta gaza kawar da yunwa da rashin aikin yi da ake fama da ita a kasar.

    Yayi alkawarin samad da ingantacciyar ayyukan cigaba da kuma tabbatar da tsaro tare da bunkasa harkar ilimi.

    Yace zai kwatanta kwatankwacin tsarin ilimi na kyauta da yayi sanda yake gwamnan Kano idan ya zama shugaba.

    Kwankwaso ya kuma yi alkawarin gina hanyoyi da gadaje domin tallafawa safarar mutane da kaya.

    October 02, 2018

    CELEBRITIES: Yadda fitattun jarumai suka raya ranar samun yancin Nijeriya

    Jarumai kama daga Sani Danja, Ali Nuhu, Maryam Yahaya, Hafsat Idris, Classiq, Nafisa Abdullahi, Rahama Sadau, Yakubu Muhammed zuwa Mansura Isa sun raya zagoyowar wannan rana.



    Ranar litinin 1 ga watan Octoba al'ummar Nijeriya sun waye gari suna murnar zagayowar ranar samun yanci, suma jaruman arewa sun raya wannan ranar farin ciki.

    Jaruman sun raya wannan ranar ta sakon da suka wallafa a shafukan su na kafafen sada zumunta.




    Cikin su akwai mawaka da fitattun jaruman masana'antar kannywood.



    Jarumai kama daga Sani Danja, Ali Nuhu, Maryam Yahaya, Hafsat Idris, Classiq, Nafisa Abdullahi, Rahama Sadau, Yakubu Muhammed zuwa Mansura Isa sun raya zagoyowar wannan rana.



    Wasu da dama sun wallafa hotuna na musamman da suka dauka na taya murnar bikin cika shekara 58 sanye da riguna mai dauke da launin kasar tare da yin ado masu jan hankali.

    Hakazalika wasun su sun kuma wallafa hotunan tutar Nijeriya a shafin su tare da rubuta sakon taya murna.
    October 02, 2018

    RELIGION: Sheikh Saeed Ibn Wahl Al-Qahtani Malamin da ya rubuta littafin 'Hisnul Muslim' ya rasu



    Babban malamin addinin musulunci, Sheikh Saeed ibn Wahl Al-Qahtani ya rasu.
    Masani kuma marubucin littafai addini ya rasu  safiyar ranar Litinin 1 ga watan oktoba a babban birnin Riyadh na kasar Saudi Arabia.

    Anyi jana'izar shi a masallacin Rajhi bayan sallar la'asar na ranar.


    Shehin malamin ya rubuta littafai da dama na musulunci. daya daga cikin litaffai da ya rubuta shine shahararren littafin addu'o'i mai suna 'Hisnul Muslim' wanda aka yi ma fassarar 'Garkuwan musulmi' da harshen hausa.

    An wallafa litaffin da harsuna daban-daban dake fadin duniya.

    Shehin Malamin ya rasu bayan ya sha fama da ciwon daji.
    October 02, 2018

    POLITICS: Mataimakiyar gwamnan Legas ta juya masa baya, tana goyon bayan abokin takarar sa

    Hakan ya fito yayin da jam'iyar APC reshin jihar take gudanar da zabe na tantance wanda zai jagoranci jam'iyar a zaben gwamna na 2019.


    Mataimakiyar gwamnan jihar Legas, Idiat Adebule, ta nuna goyon bayan ta da abokin takarar mai gidan ta na zaben fitar da gwanin jam'iyar APC.

    Hakan ya fito yayin da jam'iyar APC reshin jihar take gudanar da zabe na tantance wanda zai jagoranci jam'iyar a zaben gwamna na 2019.


    Sakamako dake fitowa daga wasu mazabu na jihar na nuna cewa gwamna Akinwunmi Ambode na fuskantar zagon kasa inda babba abokin takarar sa kuma dan takarar da mafi yawancin jiga-jigan jam'iyar ke goyon baya, Babajide Sanwo-Olu,yayi zarra.

    Hajiya Idiat ta bayyana ra'ayin ta game da wanda take goyon baya yayin da take kada kuri'a a mazabar ta dake nan Ward A na karamar hukumar Iba.

    Tace "Jam'iya ta fitar da dan takara kuma nima shi zan mara ma baya".


    Rahotanni sun bayyana cewa wasu masu yi ma mataimakiyar gwamnan hidima da  magoya bayan ta sun garzaya wajen kada kuri'a da fosta na mara ma Sanwo-Olu baya.