Ya ayyana hakan ne yayin da jirgin yakin neman zaben sa ta sauka jihar Anambra ranar Laraba 26 ga watan Satumba.
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, wanda ke neman haye kujerar shugaban kasa ya sake caccakar gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari.
Yace gwamnatin shugaban ta raba kawunan yan Nijeriya.
Ya ayyana hakan ne yayin da jirgin yakin neman zaben sa ta sauka jihar Anambra ranar Laraba 26 ga watan Satumba.
Kamar yadda Daily post ta ruwaito, dan takarar yace an samu wannan abun bakin ciki a kasar domin yan Nijeriya sun zabi wanda bai cancanta ba.
Da yake jawabi a taron da yayi da magoya bayan jam'iyar PDP na jihar Anambra, Atiku yace akwai bukatar gwamnati da sauya fasalin kasa kana ta yarda ko wacce yankin ta gudanar da alamuran shugabanci da kanta.
Ya cigaba da sukar gwamnatin APC ta yanzu inda ya bada misalin bangarorin da ta gaza samun cigaba da zai tallafa ma rayuwar yan kasa.
Ya bada misali a bangaren kiwon lafiya, harkar kasuwanci, aikin yi da kuma ayyukan walwala.
Tsohon mataimakin shugaba Obasanjo yayi kira ga yan jam'iyar PDP na jihar da su goyi bayan takarar sa na zama gwanin PDP gabanin zaben 2019.
Yayi ma al'ummar yankin kudu maso gabas alkawarin gina filin sauka da tashin jirgin sama na kasashe-da-kashe idan yayi nasarar zama shugaban kasa a zaben 2019.
Atiku yana daya daga cikin yan takara 15 dake neman lashe zaben fidda gwani na jam'iyar PDP domin fafata da yan takarar sauran jam'iyu a zaben gobe.
No comments:
Post a Comment