Jami'in binciken hukumar hana almundahana da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC, Adariko Micheal, a ranar Laraba ya bayyana abinda aka yi da kudin makaman da ake zargin Dasuki da karkatarwa.
Micheal ya ce an kashe naira 2.2 billion kan addu'ar kashe karshen Boko Haram a Nijeriya da Sauidyya, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.
Jami'in ya bayyana hakan ne yayin da yake magana a matsayin shaida a kotu a shari'ar Sambo Dasuki, tsohon mai baiwa kasa shawara lokacin gwamnatin Jonathan wanda ake zargi da wawushe kudin makamai dala bilyan biyu.
No comments:
Post a Comment