Post Top Ad

Post Top Ad

Wednesday, November 11, 2020

LET'S TALK : GYARAN TARBIYYA ( Alakar 69 Da Masu A Daidaita Sahu )

 



Da farko zan dan fadi tarihin mawakin kafin na fadi dalilin yin wannan rubutu.


Sunan sa Danieal Hernandaz. An haife shi a kasar Amurka a shekarar (8 may 1996) amma an fi saninsa da 69. Mawaki ne kuma marubuci sannan yana hip pop, ya bayyana a shekarar 2012, amma ya yi suna a shekarar 2017 bayan da ya saki wata wakarsa mai suna Gummo.




Cikakken arne ne kuma mai aikata manyan laifukka, babu irin laifin da ba ya aikatawa. Sannan kuma yana cikin kungiya ta masu tsafi. A shekarar 2018 an yanke masa hukunci zaman gidan yari na shekar 4 saboda kama shi da aika laifin zina da kananan yara, daga baya aka bada belinsa.


Ko a shekarar da ta gabata an kama shi da aikakata laifin yi wa wata karamar yarinya fyade kuma dama can ana zarginsa da laifin harka da miyagun kwayoyi, inda aka yanke masa hukuncin awa 1000hrs  a gidan yari saboda a kasarsu akwai irin wannan hukuncin.





Sannan an kuma kama shi a lokacin corona sakamakon karya dokar kulle, inda aka kai shi gidan maza kuma ya fito a ranar 4 ga watan Satumba.


Wannan mutumin cikakken dan iska ne kuma ya shahara kuma ko a Amurka ana kyamatar irinsa da masu halinsa.


DALILIN YIN WANNAN RUBUTU


Na dade ina so na yi wannan dan tsokaci amma abinda ya kuma tuna min shine yadda 'yan uwanmu masu adaidaita suka mayar da wannan mutum kamar allon rantsuwa kuma suke alfahari da saka hoton sa a jikin abin nema na kalaci, suna saka hotonsa a ko ina kamar kasan danja ta baya da gurin zaman fasinja, wasu ma ka ga sun sa a baya wajan da za ka iya hango wanda yake ciki ko kuma gaban babur din. Ya danganta.




Wai a haka sai ka cika kwaro ma kenan ko kuma babban yaro kuma da yawansu zai yi matukar wuya ka irga guda biyar baka ga wannan hoto ba kamar shi yake ba su haya ko kuma nasa ne babur din.




Ni dai a ganina da yawa basu san wane 69 ba ko kuma kawai abin nan ne na na ga wane ya sa bari ni ma na sa, ko kuma don ado.


To gaskiya wannan kuskure ne kuma ya kamata mu kyautata abin neman arzikin mu kuma mu tsaftace zukatan mu idan ya zama dole sai ka sa hoto to gwanda kasa hoton akuya ko jaki dan ya fi wannan mutumin ko a gurin Allah.


Allah ka gyara mana alumarmu ka tsabtace ta ka sa mana kishin addinin mu sannan ka sa maka gyamtar wanda baya sonka kowaye.


SOURCE : RARIYA By Abdulrahman Muhammad Sharada

(Alwazwazee)

No comments:

Post a Comment