Post Top Ad

Post Top Ad

Wednesday, November 11, 2020

RELIGION : WANI BAWAN ALLAH YA BADA FILIN SA, NA MILIYOYIN NAIRA DOMIN GINA MASALLACIN JUMA'A SABODA ALLAH A JIHAR SOKOTO

 






Alhaji Yahaya Buhari Siriddawa Babban Dan Margayi Sarkin Mallaman Sokoto Shaikh Buhari Buhari Siriddawa, ya bada filin sa na milyoyin nairori da kuma daukar nauyin gina Masallacin Jumu'ar saboda Allah da kuma sanya wa Masallacin sunan Mahaifin sa Margayi Shaikh Buhari Siriddawa.


Za'a dai fara aikin Masallacin ne da zarar injiniyoyi sun kammala zanen taswirar masallacin.


Alhaji Yahaya Buhari Siriddawa ya yi alkawarin cigaba da aikin Masallacin har ganin an kammala aikin cikin aljihun sa da yardar Allah.


Margayi Shaikh Buhari Siriddawa dai ya shafe sama da shekaru 45 yana rike da Sarautar Sarkin Malaman Sokoto. Inda ya rasu daya ga watan Azumin Ramadan da ya gabata. Wanda ya yi daidai da kwanan watan 24/4/2020.


Hakan ya sa Alhaji Yahaya Buhari Siriddawa ya yi tunanin gina masallacin Juma'ar domin zamowa sadakatun jariya ga Ruhin mahaifinsa.


Muna rokon jama'ar Musulmi da mu taya shi da addu'a domin samun nasara akan wannan aikin alheri da Alhaji Yahaya Buhari Siriddawa yake kokarin yi.


SOURCE : RARIYA BY Ahmad Bello Madunka Sokoto

No comments:

Post a Comment