Bayan gabatar wa da sifeta janar na 'yan sanda takardun korafi a kan kalaman batancinda aka yi wa manzon Allah (S A W) da hotunan Rahama Sadau suka janyo, kotu ta gindaya mata sharudda 4 da zata cika.
A ranar Litinin, NewsWireNGR sun ruwaito yadda hotunan Rahama Sadau suka janyo cece-kuce a kafafen sada zumuntar zamani, wadanda suka kai ga jarumar ta cire hotunan kuma ta bayar da hakuri.
Da yawa daga musulman arewacin Najeriya sun nuna yadda hotunan suka kawo suka ga arewa, musulunci da imaninta. Wasu kuma suka yi ta kokarin kareta.
Amma a wata takarda da wani lauya, Lawal Muhammad Gusau, ya rubuta a ranar Asabar, ya ce dole jarumar Kannywood din ta cike sharudda 4.
1. Wajibi ne lauyanta ya zama musulmi. Don ya fahimci hukuncin kotun shari'ar musulunci. Don za a yi amfani da hadisi da Arkur'ani mai girma wurin yanke hukunci.
2. 'Yan sanda za su yi aikinsu na kai ta kotun shari'a ne saboda hakkinsu ne, don a tabbatar da binciken a kan ta.
3. Sannan manyan malamai kamar Sheikh Ahmed Mahmoud Gumi da ke Kaduna, Sheikh Ahmed BUK daga Kano, Sheikh Kabir Haruna Gombe daga Gombe, Sheikh Nura Khalil daga Abuja da Sheikh All Isa Fantami, ministan sadarwa, sune malaman da za su bayar da fatawa a kan sukar manzon Allah Muhammad (SAW).
4. Mun jinjina wa Iauyoyin arewa da basu shiga cikin sabon da wani Aminu Sherif da Umar Faruk suka yi ba. Sannan ba mu bukatar ganin wani Iauya mazaunin Kaduna ya saka baki a cikin lamarin Rahama Sadau.
No comments:
Post a Comment