- A cikin satin nan wasu manyan ƴan kasuwa guda uku daga kasashen Gulf sun yi kwashe kuɗinsu zunzurutu har Dalar Amurka biliyan shida ($6,000,000,000.00) daga bankunan Faransa zuwa wasu bankunan na ƙasashen Swiss da Belgium.
- Kasar Pakistan ta soke kwangilar wasu ƙananan jiragen da ta kulla da ƙasar Faransa waɗanda kimar kuɗinsu ta kai Dalar Amurka miliyan dubu ɗaya da miliyan dari takwas ($1,800,000,000.00).
- Fitaccen ɗan kasuwar nan ɗan ƙasar Saudiyya Ahmad Ali Yazin ya soke kwangilar sayen motoci Peugeout guda 2800 ƙirar ƙasar Faransa waɗanda kuɗinsu ya kai Dalar Amurka miliyan ɗari biyu da hamsin ($250,000,000.00).
- Ƙasar Turkiya ta soke kwangilar da ta ba wa ƙasar Faransa ta ƙera makaman harbo jiragen sama waɗanda kimarsu ta kai Dalar Amurka miliyan dubu daya da miliyan dari biyu ($1,200,000,000.00).
- An ga ma'aikatan manyan shagunan Carfour mallakar Faransa da suke birjik a ƙasashen Gulf da Morocco suna ta hamma saboda babu masu zuwa sayen kayansu.
- Ma'aikatan wani babban dilan kayan Cosmetics na Faransa da ke Kuwait sun share kwanaki biyu suna loda ma motocin shara kayayyaki mallakar kamfanin ana ƙonawa.
Farawa kenan..
No comments:
Post a Comment