Post Top Ad

Post Top Ad

Sunday, September 6, 2020

NEWS : Yadda Elrufa'i Da Sanata Uba Sani Sun Kafa Tarihi A Jihar Kaduna


 

Batun harkar lafiya Sanata Uba Sani mai wakiltar Kaduna ta tsakiya a Majalisar dattijan Nieriya ya ce wa'adin mulkin Malam Nasiru Elufa'i na farko ya cimma nasarar kafa kyakkyawan tarihi ta hanyar gina cibiyoyin kula da lafiya (primary Healthcare Center) sama da dari biyu da hamisin a jihar ta Kaduna a yanzu haka. Domin baiwa harkar lafiya mahimmanci.


Sanata Uba Sani shi ma a nasa bagaren ya bayar da gudummawar kayan agaji da kayan aiki zuwa ga wani sashi na hukumar wutar lantarki PHCS. Sanatan ya kuma aminta da shirin jagoranci samar da filayen fara wani aiki na hukumar kula da kiwon lafiya ta kasa (National primary Healthcare development Agency) wanda za ta aiwatar a wani sashi da Sanatan ke wakilta.


Waɗannan ayyuka idan aka zartar da su, za su tafi ne kai tsaye don inganta cibiyoyin lantarki na hukumar PHCS da ke yankin mazabun Sanatan. Haka kuma zai ƙarfafa wasu sashi na ma’aikatar lafiya.


Cutar Corona Virus cuta ce wacce ta girgiza tattalin arzikin duniya. Haka kuma ta saka cbiyoyin kiwon lafiyar Nijeriyar cikin wani yanayi mai tsanani.


Abin sha'awar anan shine motsi na farko da Sanata Uba Sani yayi shine cikin gaggawa ya dauki nauyin gabatar da kudri a majalisar dattijai watan Yulin 2019, inda ya bukaci majalisa da ta umarci kwamitin ta na kiwon lafiya tare da Babban Daraktan Cibiyar hana yaduwar Cututtuka na hukamar (NCDC) akan cimma matsaya na dokar samar da cibiyoyin yanki-yanki a duk yankunanmu shida da muke da su a Nijeriya tare da samar da ofisoshi a duk jihohin Nijeriya.


Kudrin na Sanata Uba Sani wanda tuni Majalisar Dattawan ta zartar da shi, ta kuma yanke shawara cewa ya kamata a samu kari cikin kasafin kudin don gudanar da aikin hukumomin na NCDC da NPHCDA don basu damar cimma burinsu na kawo karshen cutattukan.


Bugu da kari Sanata Uba Sani ya dauki nauyin wani kudirin domin samar da cibiyar kula da lafiya ta tarayya a Rigasa Kaduna, (Federal medical Center Rigasa Kaduna). Wanda yanzu haka kudirin yana majalisar ana kan bin ka'idojin rahotan yarjewa.


Burin Sanata Uba Sani shine kawo karshen matsalolin jihar Kaduna da ma Arewacin Nijeriya baki daya.


Sanatan ya rubuta wannan labari ne a cikin littafinsa na cika shekara daya a Majalisar Dattijai.

SOURCE : Hamisu Muhammad

No comments:

Post a Comment