Gwamnatin tarayya ta fara shirye-shiryen bayar da agaji ga ƙauyukan arewa maso gabas ta hanyar amfani da jiragen sama domin cilla wa 'yan gudun hijira abinci.
Ministar kula da ayyukan jin-ƙai da kare afkuwar bala'i Sadiya Farouk, a ranar Lahadi ta shaida wa 'yan jaridu a Maiduguri cewa za a fara amfani da jiragen sojojin sama a Nijeriya domin cilla abinci da sauran kayayyakin tallafi kamar bargo da dai sauransu ga 'yan gudun hijirar da ba sa gidajensu.
Ta bayyana cewa akwai matsaloli da ma'aikatan bayar da agaji ke fuskanta na kai wa ga jama'ar da ke cikin ƙauyen kaya, inda ta ce cilla abincin ne mafita ga ƙauyukan da mota ba ta iya zuwa.
No comments:
Post a Comment