Dole Mu Tashi Tsaye Don Ganin Mun Farfado Da Martabar Jihar Katsina, Cewar Musa Abdullahi
Ba mu jin dadin abinda ke faruwa a jihar Katsina na tone-tone
Daga Jamilu Dabawa, Katsina
Shugaban Zauren Mutanen Jihar Katsina, Alhaji Musa Abdullahi ya bayyana cewa halin da Jihar Katsina ta samu kanta, kowa na da rawar da zai taka, don ganin jihar Katsina ta dawo martabarta a idon duniya kamar yadda aka santa.
Musa Abdullahi ya bayyana haka ne, lokacin da ake kaddamar da zauren mutanen jihar Katsina watau (Katsina Peoples Forum) a karon farko, wanda ya gudana a dakin taro na Katsina Motel.
Shugaban taron, wanda ya taba zama Shugaban Hukumar Gudanarwa Ta Jami'ar Umaru Musa Yar'adua, da ke Katsina ya kara da cewa dalilin wannan taro shi ne mu maido mutuncin da martaba Jihar Katsina kamar yadda aka santa ta a da fannin ilimi da tattalin arziki da zaman lafiya da kuma yanayin zamantakewa.
Abdullahi ya ci gaba da cewa akwai abubuwan da ke faruwa a kwanakin nan, wanda duk dan asalin jihar Katsina bai jin dadinsa, maimakon a bar shi kara-zube, muka ga ya dace mu zauna don ganin an samu masallaha. So muke a tafi alkibla guda, ba mu jin dadin wannan tone tone na Mahadi ko gaskiya ne ko akasin haka. Zaman mu nan da yardar Allah abubuwa za su fara canzawa. Kuma komai mutum ke yi mai kyau da marar kyau ya sani. Gwamnan nan zaben shi jamaa suka Yi, akwai yan majalisa an zabe su domin takawa bangaren zartarwa burki, abar yan majalisa su yi aikin su.
Shima da yake nasa jawabi daya daga cikin mahalartan taron injiniya Muttaka Rabe Darma ya bayyana cewa, bai kamata mutane masu ilimin Jihar Katsina su zauna, suna kallon mawuyacin halin da Jihar Katsina da arewa suke ba. Muka ya dace a fito da wani tsarin na masana don ganin an fita daga cikin wannan hali. Yanzu haka akwai farfesoshi da yan kasuwa domin Jihar Katsina da arewa ta koma yadda aka santa. Bayan tafi yanzu kyau, za mu aiki tukuro don ganin mun fitar da Jihar Katsina da matsalolin rashin tsaro da tattalin arziki da Nima da kuma zamantakewa. Kowacce matsala tana da magani, Kuma insha Allah wannan zaman zai haifar da da Mai ido.
No comments:
Post a Comment