Gwamnatin Tarayya ta fitar da rahoton cewa ta kashe naira bilyan 31 wajen yaki da dakile cutar Coronavirus a cikin watanni hudu.
Wannan bayani ya na kunshe ne a cikin wata takarda da Babban Mai Binciken Kashe Kudade na Kasa, Ahmed Idris ya aika wa Kungiyar SERAP da ta nemi sanin adadin kudaden da gwamnatin tarayya ta kashe wajen yaki da cutar Coronavirus.
A ranar 10 Ga Agusta ne SERAP tare da CODE suka aika wa Ofishin AGF wasikar neman sanin kudaden da aka kashe da kuma sanin bayanan adadin wadanda aka raba wa tallafin jinkai a kasar nan.
Idris ya maida wa SERAP da CODE amsa a ranar 4 Ga Satumba, inda ya bayyana cewa an kashe naira bilyan 31 daga ranar 1 Ga Afrilu zuwa 31 Ga Satumba.
An tara gudummawa daga jama’a da kamfanoni ta kudi naira bilyan 36.3. An kashe naira bilyan 30.5 daga Afrilu zuwa Agusta. A yanzu akwai sauran naira bilyan 5.9 ajiye a Asusun Kudaden Fatattakar Korona.
Daga cikin kudaden, Kwamitin Yaki da Cutar Korona da Shugaba Buhari ya kafa, ya kashe naira bilyan 22, jihohi 36 sun kashe naira bilyan 7.
SOURCE : Comr Abba Sani Pantami
No comments:
Post a Comment