Post Top Ad

Post Top Ad

Sunday, September 6, 2020

NEWS : Buhari Zai Shilla Kasar Nijar A Gobe Litinin

 



Shugaba Muhammadu Buhari zai shilla kasar Nijar a gobe Litinin domin halartan taron shugabannin kasan yankin Afrika ta yamma karkashin gammayar ECOWAS.


Mai magana da yawunsa, Malam Garba Shehu, ya bayyana hakan ranar Lahadi, a shafinsa na Tuwita.


Ya ce Buhari zai samu rakiyar manyan ministocinsa kuma zai dawo bayan zaman.


Garba Shehu yace: "Shugaba Muhammadu Buhari zai tashi daga Abuja zuwa Niamey, jamhurriyar Nijar domin halartan taron gangamin shugabannin kasar yankin Afrika ta yamma ECOWAS karo na 57.


A taron da za'ayi cikin kwana daya, za'a tattauna kan rahoto na musamman kan COVID-19 da shugaba Buhari zai gabatar bayan nadashi zakaran yaki da COVID-19 a taron yanar gizon da akayi ranar 23 ga afrilu, 2020.


Hakazalika za'a tattauna kan lamarin ta'addanci, barandanci da kuma juyin mulkin da Sojoji sukayi a kasar Mali.


Source : Comr Abba Sani Pantami

No comments:

Post a Comment