A jiya litinin ne Gwamna jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari ya Gabatar da daftarin Kasafin kudin shekarar Mai kamawa ta 2019 a gaban zauren majalisar dokoki ta jihar Katsina, domin samun Amincewa su kamar yadda dokar kasa ta tanada.
Kasafin kudin Mai taken “Kasafin Daidaita Lamurra” da Gwamna ya Mika an kiyasin kashe naira Biliyan dari biyu da dubu dari bakwai. Inda manya ayyuka za su lakume zunzurutun kudi har naira Biliyan dari da arba’in da takwas, Wanda shi ne Kashi sabain da ukku na jimlar Kasafin kudin. A ya yin da su Kuma ayyuka na yau da kullum ake sa ran kashe tsabar kudi har naira biliyan hamsin da biyu wato kudaden albashi da tafiyar da gwamnati
Gwamna Masari ya cigaba da cewa bangaren ilimi kusan Kashi Sha Tara na jimlar kudaden manyan ayyuka da Biliyan Sha Tara, maaikar lafiya Biliyan ashirin maaikatar gonna Biliyan goma, ayyukan hanyoyi Biliyan ashirin. Sai Kuma maaikatar ruwa biliyan goma Sha biyu, maaikatar muhalli biliyan ashirin da hudu wadda ita ce wadda tafi samun kaso Mai tsoka a cikin wannan kasafi.
Da yake maida jawabi kakakin majalisar dokoki na jihar Katsina, Abubakar Yahya Kusada ya ce majalisar za ta bada dukkanin goyan bayan da ya dace, domin ganin ya samu Amincewa cikin lokaci. Ya Kuma Kira ga maaikatu da hukumomi gwamnati da su bayar da hadin Kai ga kwamitocin majalisar, da za su jagoranci Kasafin kudin. Shugaban majalisar ya jinjinawa Gwamna Aminu Bello Masari bisa ga Amincewa da ya Yi da dokar Nan da shugaban kasa Muhammadu buhari ya Sanya hannu a kwanakin baya, inda ita jihar Katsina ta amince majalisar za ta Zama Mai cin gashin kanta kan kudi
No comments:
Post a Comment