Post Top Ad

Post Top Ad

Wednesday, October 31, 2018

NEWS: Sai Mun Tarwatsa Jihar Zamfara Baki Daya,Cewar ‘Yan Ta’adda



‘Yan ta’addan yankin Zamfara (Barayin Shanu, ko masu Garkuwa da mutane), wadanda suka addabi jihar sunn juya akalarsu gadan-gadan a Karamar Hukumar Mulki ta Zurmi.
A mako guda sun kai mummunan hari a garin Dauran, inda suka dauke ‘yan mata biyu (‘yan biyu da ake shirin aurensu ba da jimawa ba). Sun yi garkuwa da mutum uku a Birnin Tsaba. Sun kuma kara garkuwa da wasu a Dauran. Sun kashe mutum shida ciki har jami’in ‘Yan Sanda a Gurbin ‘Bore. Bayan Kone dukiya da motoci da shaguna. Duka a yankin Karamar Hukumar Zurmi, a wannan makon.

Bayan wannan, barayin sun kara shigowa da wani sabon salo na bala’i, wanda idan suka yi garkuwa da mutum, idan namiji ne ko mace, to sai sun yi kokarin bata mishi rayuwa, ta hanyar yin luwadi da shi, in mace ce su yi zina da ita.

Yanzu haka barayin sun sanya wa dajin da suke ajiye mutane idan sunyi garkuwa da su suna; “ZAMFARA SAMBISA”.
Muna kira zuwa ga wadanda hakkin kare mu yake a kansu, su sani mu Zamfarawa muna cikin tashin hankali da rashin kwanciyar hankali, wanda har ya kai yanzu barayin sun karbe wani yanki a jihar Zamfara, idan kaddarar Allah ta sanya kana zaune a yankin, ko kana aiki a yankin, to baka da natsuwa da walwala.
Allah muna rokonka, ka kawo mana agaji a jihar Zamfara.

No comments:

Post a Comment