An bayyana cewar rashin samun ilimin addinin Musulunci yadda ya kamata shine ke haifar da samuwar 'yan ta'adda musamman a yankin Arewacin Najeriya.
Shugaban kungiyar Izala na ƙasa baki daya Imam Abdullahi Bala Lau ya bayyana hakan lokacin wata ganawa da ya yi da manema labarai a Kaduna.
Sheikh Lau ya ƙara da cewar a halin yanzu Ƙungiyar ta su za ta mayar da hankali sosai wajen yin da'awa da karantar da Fulanin Daji da ke rayuwa a rugage, kasancewar yadda ake yawaitar samun 'yan ta'adda da masu garkuwa da mutane a cikin su a wannan zamani.
"Haƙiƙa ilimin addinin Musulunci shine ke gyara rayuwar al'umma, ya mayar da su bisa tsari, muna da yakinin muddin muka juya ga bangaren ilimantar da Fulani Makiyaya addini, babu shakka za'a samu nasara wajen daƙile yaɗuwar ayyukan ta'adda a Najeriya".
Ya ƙara da cewar wannan shine babban dalilin da ya sanya Ƙungiyar mayar da hankali sosai wajen bunƙasa ilimi, wannan ya sanya suka yi kokari wajen gina jami'a a Jihar Jigawa, da ƙoƙarin da suke yi yanzu a Jihar Sokoto na aikin ginin Jami'a wadda tsohon Gwamnan Jihar Bafarawa ya ba su.
Babban malamin ya yi kuma tsokaci dangane da taron da kungiyar tasu ta kira 'ya'yanta a Kaduna, inda yace sun kira taron ƙarawa juna ilimi ne karo na farko tun bayan ɓullar cutar CORONA, domin su fahimtar da su yadda za su cigaba da gudanar da'awa bisa ga tsari da kaucewa cunkoso kasancewar Ƙungiyar ita ce kan gaba a Najeriya wajen tara Miliyoyin mutane.
Daga ƙarshe shugaba Abdullahi Bala Lau, ya bayyana cewar Ƙungiyar tana wani shirin ilimantar da jama'a akan batun bada bashi mara ruwa, da babban bankin Najeriya zai bayar, inda ya bayyana cewar Izala ta shigo ciki domin fadakar da al'ummar Musulmi hanyoyin da za su bi wajen cin gajiyar bashin.
No comments:
Post a Comment