Post Top Ad

Post Top Ad

Wednesday, September 9, 2020

NEWS : Da mu rasa Karnukanmu gara iyayenmu Mata su mutu – Mafarauta a Kano

 



Da mu rasa Karnukanmu gara iyayenmu Mata su mutu – Mafarauta a Kano


Wani mafarauci mai suna Ado Muhammad Maiduna ya bayyana cewa da yawa mafarauta da su rasa karnukansu gara a ce sun rasa uwar da ta haife su.


Ado Muhammad Maiduna ya bayyana haka ne a lokacin da ƴan bijilantin unguwa Uku da ke ƙaramar hukumar Tarauni, su ka samu nasarar kuɓutar masa da karensa bayan da aka sace shi.


“Magana ta gaskiya ba wai a yankin Unguwa Uku ba, duk inda wani mafarauci ya ke to babu abin da mu ka tsana kamar a sace mana Kare, domin wani mafaraucin ya gwammace ya rasa mahaifiyarsa akan ya rasa karen sa”


“Karnuka su na daraja sosai, domin farashin Kare yana kai wa naira 25,000 zuwa naira 30,000″ in ji Ado Maiduna.


Ya ƙara da cewa Yara suna sace musu karnuka tare da sayar da shi akan abin da bai wuce naira 3,000 zuwa 5,000 ba.


A nasa ɓangaren shugaban ƴan bijilantin unguwa Uku Dauda Isma’il, ya bayyana cewa sun kama wasu matasa guda biyu, Ciyalle da Abba, waɗanda su ka same su da karnuka guda 3 ciki har da wani kare da ya samu horo na musamman mallakin wani jami’in soji.



Ya ƙara da cewa bayan da su kama yaran ne, sai su ka garzaya da su zuwa chaji ofis din ƴan sanda.


“Mun kai su chaji ofis din ƴan sanda tare da waɗanda karnukan su ke mallakinsu ne”


“Tun da farko sojan da aka sacewa kare ya yi niyyar kiran ƴan uwansa sojoji daga bariki da nufin daukar mataki akan waɗannan yaran da ake zargin sun sace karnukan, amma sai mu ka ba shi baki akan a je gurin ƴan sanda”


“Wannan soja ya bamu hadin kai tare da bayyana gamsuwarsa akan hakan”


A ƙarshe Dauda Isma’il ya yi kira ga mazauna Unguwar ta Unguwa Uku da su cigaba da ba su hadin kai domin ganin an kawo ƙarshen aiyukan da ba su dace a fadin Unguwar.

No comments:

Post a Comment