Post Top Ad

Post Top Ad

Wednesday, August 15, 2018

NEWS: Za A Yi Bikin Bajakolin Sana’o’i Da Karrama Muhimman Mutane A Kano



Gidauniyar Shehu Usman (Shehu and Associate) tare da hadin guiwar Cibiyar dakin taro ta Afrika Anchor da ke Ado Bayero Mall, kan titin zuwa gidan namun daji (Zoo Road) sun shirya tsaf domin gudanar da bikin nuna kayan sana’o’i da nau’ikan abinci tare da karrama wasu fitattun mutane daga sassan jihohin Nijeriya.

Duk da cewa Kungiyar ta Shehu Usman sun shirya taruka da dama a baya, ana iya cewa wannan taron shi ne irinsa na farko da hadakar kamfanonin biyu suka shirya.

Za a yi wannan taro ranar alhamis 16 ga watan Agusta da misalin karfe 8 na safe in da za a fara da bikin bajakolin kayan sana’o’i da abincin gargajiya da na zamani kuma za a baiwa kowa dama ya shiga don kashe kudinsa da kwarkwatan idanunsa, za a ci gaba da gabatar da wannan bajakoli har zuwa karfe biyar na yamma.

Daga nan za a shiga sha’ani na biyu wato bikin karrama fitattun mutane wadanda suka bayar da gudunmuwa a cikin al’umma ta fannoni daban-daban wadanda za a karrama sun hadar da:-

Masu Shirya Fim din Hausa, ‘Yan wasan tamaula(Kwallon kafa) ‘Yan siyasa da yan kasuwa.

Cikin wanda za a karrama akwai shahararren dan kwallon kafar Nijeriya Ahmad Musa da tauraron wasan kwaiwayon Hausa Ali Nuhu da mawakin siysa Dauda Kahutu Rarara da sauran muhimman mutane. Mawallafin SARAUNIYA wato Maje El-Hajeej Hotoro na daga cikin wadanda za a karrama.

Kada a manta a wannan zango akwai kudin shiga naira dubu biyu(N2000) ga matsaikata da kuma naira dubu biyar (N5000) ga ajin farko.

A zantawarta da manema labarai shugabar kungiyar Shehu Usman Hajiya Maryam Yunusa ta ce “manufar shirya taron dai ita ce don fito da nagartattun mutane masu taimakawa al’umma a fannoni da dama da kuma karfafa musu guiwa tare da fito da kayan abincinmu na gargajiya da sauran sana’o’inmu na hannu”.

Taken taron dai na wannan shekara shi ne Daren Shahara(Night Of Fame)

#Rariya

No comments:

Post a Comment