Post Top Ad

Post Top Ad

Wednesday, August 15, 2018

NEWS : Budurwa Ta Yanke Mazakuta Wani Ma’aikacin ‘N-Power’ A Jigawa



Lamarin Ya Auku ne A Karamar Hukumar Babura Dake Jihar Jigawa, Inda Wata Budurwa Mai Suna Ramatu Tafida ‘Yar Shekaru 17 Ta Yanke Mazakutar Saurayinta Mai Shekaru 25 Mai Suna Abdulahi Sabo. Wanda Yake Aikin N-power.

Budurwa Ta Zargi Saurayin Nata ne Da Bata Mata Rayuwa Ta Hanyar Saduwa Da Ita, Da Zummar Zai Aure ta Wanda Daga Bisani Ta Sami Labarin Ya Fasa Auren Nata.

Ramatu Ta Bayyana Dalilin Da ya sa Ta Aikata Wannan Aika-Aika, Inda Ta ce Abdullahi Ya Yaudare ta Ya santa A Matsayin ‘Ya Mace, Sai Daga Bisani Ta Sami Labarin Ya Fasa Aurenta, Ya Samu Wata Daban.

An Garzaya Da Abdullahi Asibitin Aminu Kano, Domin Neman Mafita, Sai Dai Yace Har yanzu Yana Mugun Sonta, Amma Asiri Ta yi masa A Lokacin Da Ta Yanke Masa Mazakuta.

Tuni Jami’an Civil Defence, Suka Cafke Ramatu Domin Gudanar Da Bincike.

No comments:

Post a Comment