Post Top Ad

Post Top Ad

Sunday, June 10, 2018

Shin Muhamad Salah Zai Yarda Ya Koma Barcelona



A halin yanzu, kungiyar kwallon kafa ta Barcelona na zawarcin ɗaya daga cikin zakarun kwallon kafa wato Muhammad Salah.

Dan wasan ɗan asalin kasar Masar ne, kuma yana da shekaru 25 da haihuwa. Salah ne ya zamo zakara a gasar Premier din bana. Ya tsere wa takwarorinsa yan wasa, inda da ya jefa kwallaye har 32 a ragar abokan hamayya. Haka ma a gasar cin kofin zakararun turai, Salah ya kokarta sosai. Kodayake ya samu matsala lokacin gudanar da wasan karshe, inda ya raunata, daga bisanu aka fitar da shi daga wasan tun kafin a je hutun rabin lokaci.

Abin tambayar a nan shi ne: Anya kuwa liverpool za su amince su sayar da Muhammad Salah ga Barcelona?

No comments:

Post a Comment