Post Top Ad

Post Top Ad

Sunday, June 3, 2018

Buhari Ya Tabbatar Da Cewa Shi Na Matasa Ne, Cewar Hajiya Ummi Suleiman



“Ni sunana Hajiya Ummi Suleiman
Uwar kungiyar Sudasa Charity Foundation, wacce aka fi sani da Uwar Marayun Adamawa.

Ni dai ina goyon bayan shugaba Muhammadu Buhari sama da shekara goma kuma tunda ya hau mulki ina farin ciki matuka kuma ina jin dadi a duk lokacin da na ji ya kawo mana ci gaba a kasar mu Nijeriya.

“Haka kuma ina mai mika godiya zuwa ga shugaba Buhari akan namijin kokarin da yake yi wurin ganin ya kawo cigaba, da kuma rantama hannun da ya yi akan dokar baiwa matasa damar tsayawa takara (Not too young to run). Wannan ba karamin ci gaba bane a kasar nan, wanda a nahiyar Afrika babu kasar da ta karu da doka na cigaba kamar haka.

“A Nijeriya muna tattare da matasa masu ilimi da fasaha, wannan shine lokacin da za su fara baiwa kasar su gudunmawa, wanda hakan ya ba su damar tsayawa takara daga shekarar 2019.

“Kuma ina kira ga matasa da su yi koyi da irin adalci, kishi da son ci gaban kasanmu Nijeriya kamar yadda shugaba Buhari yake yi. Kuma ku zamo jagorori wadanda mu iyaye mata za mu yi alfahari da ku kuma wanda kannenku za su yi koyi da ku idan sun taso.

“Haka kuma ku bada himma da kokari wurin ganin mun dawo da shugaba Buhari kan karagar mulkinsa a zaben 2019 domin ci gaban matasa, mata da kasa baki daya”.

#Rariya

No comments:

Post a Comment