Post Top Ad

Post Top Ad

Wednesday, November 11, 2020

LET'S TALK : SAMA DA KASHI 14 NA YAN NIGERIA NA SHAN TABAR WIWI ( WEED )

 




Gwamnatin Najeriya ta ce sama da  14 da rabi na al’ummar kasar na shan wiwi ko hodar ibilis ko kuma kodin da ke tagayyara hankalinsu.


Daraktar da ke Yaki da Masu Amfani da Haramtattun Kwayoyi a Hukumar NDLEA Titus-Awogbuyi Joyce ta sanar da haka sakamakon alkaluman da hukumar ta tattara a shekarar 2018.





Jami’ar ta ce, alkaluman sun kuma bayyana cewar, daga cikin mutane 4 da ke ta'ammuli da wadannan miyagun kwayoyi guda mace ce, abin da ke nuna yadda matsalar ta shafi kowanne bangare.




Hukumar Yaki da Amfani da Miyagun Kwayoyin na Majalisar Dinkin Duniya ta ce mutane miliyan 246 suka yi amfani da irin wadannan kwayoyi a duniya daga shekarar 2014.




Ministan Kasafin Kudin Najeriya da Tsare-Tsare, Prince Clem Ikanade Agba ya ce matsalar na yi wa kasa matukar illa wajen ci gabanta.



No comments:

Post a Comment