Post Top Ad

Post Top Ad

Saturday, September 5, 2020

NEWS : SARKIN KANO SANUSI || Buhari Ya Yi Daidai Da Ya Cire Tallafin Man Fetur, Yanzu An Samu Karuwar Gaskiya Cikin Hukumar NNPC

 





Tsohon sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II, ya ce abin da gwamnatin tarayya ta yi wajen farfado da tattalin arzikin kasa ya yi daidai.


A karshen makon nan ne aka rahoto tsohon sarkin ya na cewa tun kafin a gamu da annobar COVID-19, ya kamata gwamnati ta dauki wadannan matakai.


Da ya ke magana a gidan talabijin Arise TV a ranar Juma’a, 4 ga watan Satumba, Sanusi II ya ce cire tallafin man fetur da aka yi, shi ne abin da ya dace.


Wadansu matakai da ake dauka kwanan nan, wadanda aka aro daga IMF na cire tallafin man fetur, duk da zafin yin hakan, su ne abubuwan da su ka dace ayi idan ana so kudin asusun gwamnati su karu.


Sanusi II ya kara da cewa: “Yanzu an samu karuwar gaskiya a hukumar NNPC.


Na ji cewa NNPC ta zuba kusan Naira tiriliyan biyu a asusun FAAC, wanda wannan ya fi abin da aka tara a tsawon shekaru.


Mai martaba ya ke cewa idan aka samu gaskiya wajen sha’anin mai, za a ga canji a sauran bangarorin gwamnati.


RAYOYIN MUTANE 


Shamsu Bello : Aiki daya zuwa biyu ya ragewa mai girma shugaban kasa wa innan mahimman ayyuka sune kamar haka

1 cire tallafin ruwan sama

2 cire tallafin iskar da mutane suke shaka

Idan har gwamnati tayi wannan namijin kokari hakika zata farfado da tattalin arzikin Nigeria kuma zata samu Karin kudaden da zata saka acikin asusun gida Dana waje.

Ali Muhammad Ali Mustapha : Sai yanxu mukagane ganduje mutunne Mai hangen nesa Allah yaci gabada nesantaka da duk wani abuda yashafi mulkin kasarnan daga appointment na siyasa da kuma duk wani mukamin gwamnati Allah yayiwa ganduje albarka da yaraba matsiyaci da saruta kuma haka xaka kare bakar xuciyarka da,muguntarka ba avinda xakasake xama da yardar Allah (S,W,T,) tir da irin halinka aniyyar kowa tabishi.


Sani Saleh Muhammad : Ai Kai dama baka da ehmani talakawane kawai suke Sanka Kai baka sansu da good luck Jonathan yakara kudin Mai da bakinka kashiga kafafen yada labarai kana bawa yan Nigeria hukuri suyi hakuri da Karin da akai indai suka hakura shekarah biyu wllh kowa sai yaji dadi kaikaifadi wanan da bakinka a freedom redio kano kuma gashi haryanxu shirru mukeji kamar anshuka dusa yanxu kuma kace gwamnatin tarayya tayi dai dai kaifa attajirine har aka gama lok down na curona wannan tallafi kacire a aljihunka kabawa talakawa hmm Allah yasa mudace.


Bashir Sani Umar  : mlm Muhammad sunusi na ll Allah ya qr mk lpy, ya kawo maka canji mafi alkairi a rayuwarka, may be fitowar wannn magana dg bakinka zata rage yawan zage zage da ake yiwa shugaban kasar mu mai albarka dg bakin 'yan ta more, Allah ya gyara mana kasarmu Nigeria y kawo mn canji mafi alakairi.


Fatihu Sani :  Allah ya qarawa maigirma Sarki nasara.Wannan bayanan naku ne ku Manya.Wanda ke zuwa Lagos a dubu bakwai an bayar da shi 15k.Me zuwa Skk 2k an mayar 4k,ta yaya ze gane wannan yaren na yan boko?Kuma shi an gaya masa a lokacin da yake sayen sa a 84 Gwamnatin Cin hanci da idanu da rashawa ce.Kuma lokacin da ake so ya bada kuri'a ba'a gaya masa cewa akwai wani Abu wai shi NNPC ana cuwa cuwa acikin ta,idan akayi abinda ze qara masa tsanani,shikenan ya kawo masa canji ba.



No comments:

Post a Comment