Post Top Ad

Post Top Ad

Saturday, September 5, 2020

NEWS : MARTANI AKAN WASU WAWAYEN CIKIN MU (Gentle Zeey)

 




Jama'a ya kamata mu dawo cikin hankalin mu kuma kada mu manta cewa Allah zai tsaida mu ya yi mana hisabi akan abinda harsunan mu suka furta mai kyau da marar kyau.


Hanan Buhari dai ba ita muka zaba a matsayin shugaban kasa ba kuma ba ita take mulkin ba, masu neman debewa auren ta albarka ya kamata ku yi wa kanku adalci ita ma kuyi mata.


Shin don Allah menene laifin ta?

Dama laifin wani yana shafan wani ne?


Ina so mai wannan mummunar fata ya ji a ransa idan shine a matsayinta ya zai ji?


Fata nagari...


RA'AYOYIN MUTANE


Abubakar Hassan Alarima   Kaji wata yar'maula fah, to ai kece wawiyar, saboda duk wanda akacemasa aniyarka tabika yayi fada ko yaji haushi to aniyar tasa ba mai kyau bace. Ance Allah yasa mijinta yayi irin halin babanta Buhari ku kuma kunce bahaka yakamata ace ba, to so kuke ace Allah yasa mijinnata yayi irin halin Fir'auna?


Galadima Allau Ashe dama ubanta chutar Nigeria yake kenan Allah Yasa Mijinta Yariketa Da Zuciyar da ubanta yake Rikon Nigeria Yayimata Kulawa kamar yanda Yakulada yankin Arewa musamman yankin Zamfara Katsina Sokoto da kebbi da Kaduna Da Borno da Nasarawa.

Tijjani Musa Tijjani wannan Gaskiyane gentle zee, kuma wanda yasan mutumci iyayensa bazai zagi iyayen wani ba. duk wanda kaga yazagi uban wani daman baidar ubansa ma. Hanan Buhari Allah yasa albarka a Aurenta dama sauran duk sauran masu Aure dama wanda zasuyi gaba.

halin da muke ciki acikin wannan kasar tamu Nigeria Allah yakawo mana sauki da mafita.


Tasiu M Rufai Gumel To meye abin damuwa acikin wanan lamari nifa Wlh banga wani abun damuwaba, Don ancewa mutum aniyarsa ta bisa ai bekamata ya damuba. Sai dai idan mutun yasan bashi da kyakyawan niyya akan Al'umma, Don Allah ya kamata muke Yiwa junanmu kyakyawan zato.


Mustapha Maichaji Fce Ktn Allah yasa yadda baban ta yaso mijin ta ya sota haka, ashe yin alkhairy yana da dadi irin kyautata da kulawa da tausayin talakawa da yayi Allah yasa mijin ta shima yayi Mata haka, yadda muka Sha JAR MIYA itama Tasha harda nama.

No comments:

Post a Comment