Post Top Ad

Post Top Ad

Thursday, October 11, 2018

RELIGION: An sake samun limamiya mace a Turai, jiya tayi bayanin matsayinta ga 'yan jarida

- Limamiyar mata ta farko a kasar Denmark ta jagoranci masallacin mata sallah
- Mai neman hakkin musulmai ce da kuma hadin kan mata 
- Khankan ta jagoranci masallacin Mariam dake Copenhagen, wanda dama mata ke jagorantar shi 





Limamiyar farko ta mata wacce ta jagoranci kungiyar masallacin mata dake Copenhagen mai suna masallacin Mariam. Mai kwato hakkin musulmai ce a abubuwan da suka danganci hadin kan mata. Tayi rubuce rubuce akan musulunci da siyasa a rayuwa. Khankan haifaffiyar kasar Denmark cewa 1974, mahaifiyar ta yar kasar Finland, mahaifinta kuma Dan Syria. Khankan tayi karatu a Damascus inda ta dawo Denmark a 2000. Tana da digiri na biyu a fannin zamantakewar addini da digirin digirgir daga jami'ar Copenhagen. Masallacin da take jagoranci ya sha bambam da sauran masallatan Denmark saboda shi mata ke jagorantar shi. Akwai ire iren masallatan a US, Canada da Jamus 

Khankan ta kirkiro kungiyar mai suna 'Critical Muslims' wacce ke da burin alakanta addini da siyasa. An bude masallacin ne a watan Fabrairu Amma bai fara aiki ba sai watan Augusta. Khankan ke Kiran sallah inda mata 60 ke binta. Sabon masallacin ya daura aure masu yawa. Suna daura auren mutane masu bambancin addini, wanda wasu masallatan basa yi. 




No comments:

Post a Comment