Dan kwallon Nijeriya, Abdullahi Shehu ya yi kira ga Gwamnatin jihar Sokoto ta sanya ofishin Kwamishiniyar al’amuran mata ta jihar da ta ci gaba da kokarin da ake na kauda shaye-shaye da ya yi kamari a cikin mata a jihar Sokoto.
Ya ce mata sune iyaye da suke koyarda tarbiyya da idan aka dorawa ofishin Kwamishiyar matan wannan nauyi zai taimaka sosai wajen dakile wannan matsala da take samun karbuwa a tsakanin Mata da matasa a jihar nan.
Ganin cewa mata sune iyaye da suke da kokari da ba wani da zaizo musu ya basu wani abu su yarda dan a cutar da al’umma.
Abdullahi A Shehu, wanda yake wasa a kungiyar Busaspor dake kasar Turkiya, ya kara da cewa saboda damuwa da kokarin yadda za a taimaka dan kauda matsalar shaye-shayen zai bude wata cibiya a Sokoto da za ta rika bada shawarwari ga masu ta’ammali da kwayoyi kan illar da take haifarwa domin su daina.
Ya ce anan matakin jihar Sokoto a kananan hukumomi 23 dukkanin Shuwagabannin kungiyar za su rika zuwa dan zakulo wasu daga masu shaye-shayen inda za’a rika basu shawarwari akan illar shan kwayoyi.
Ya kara da cewa sun fahimci cewa yawanci shaye-shayen anfi samun mata masuyi a tsakanin wasu kananan hukumomi dake kwaryar Birni Sokoto da suka hada da Ilella, bodinga,Dange Shuni, Wurno da Birni da kewaye,wanda sun samo masu irin wannan shaye-shaye kuma an basu shawarwari da tasa da dama sun daina kuma sun koya musu sana’oi da basu jari.
Babban kudurin Abdullahi A Shehu shine Mata su sami ilimi su tsaya da kafunsu su bada tarbiyya ga al’umma,amma idan mace mai shaye-shaye ce bazata zama abin koyi da bada tarbiyya ga al’umma ba.
Abdullahi A Shehu yace akwai shirin yin wani gagarumin gangami a cikin wannan watan dazai hada Mata iyaye da matasa dan wayar musu dakai kan illar shaye-shayen miyagun kwayoyi.
Yace yawanci masu shiga harkar shaye-shaye ana jansu ne,tun suna kanana,wasu kuma matan damuwa da bakin ciki ne ke jefasu cikin harkar wasu kuma samari su yaudaresu dan su rika gusar musu da hankali suna abinda bai kamata ba dasu.
Abdullahi A Shehu yace shaye-shaye wani abune da da dama mutane kan yi Kota shan kwayoyin nan yau da kullum da wasu suke da nufin shan maganin gajiya wanda nau’i ne na shaye shaye wanda shi ma illa ne sosai.
Ya kara da cewa alhakin kowa da kowa ne a cikin al’umma yasa hannu dan kauda wannan illa ta shaye-shaye ,wanda masu safarar kwayoyin nan su suke shigowa dashi Sokoto suna rabawa har ake kaiwa ga matan aure a gidaje.
Abdullahi A Shehu yace babban sakonda suke isarwa ga mata dazasu kawo dan basu shawarwari, akan su daina shaye-shaye shine da farko za’a tunatar dasu akan suji tsoron Allah tare da nuna musu illar shan kwayoyi,kuma su dubi kansu a matsayin iyaye da zata bada tarbiyya ga yara da zata haifa su zama nagari a al’umma.
A Shehu yayi kira ga dukkanin masu ruwa da tsaki a jiharnan su tashi tsaye dan ganin an dakile shigowa da kayan shaye-shaye cikin jiharnan dan har takai ana cewa ita ce kan gaba a harkar shaye-shaye. Ta yaba da irin kokarinda Mai martaba sarkin Sokoto Alhaji Muhammad sa’adu Abubakar III keyi wajen ganin an kauda wannan matsala data shafi al’umma.
Daga Aliyu Hungumawa Sak
No comments:
Post a Comment