Tun hawan shugaban kasar Amurka, Donald Trump, karagar mulki a shekarar 2016, wani sabon abu ya fito a kasar musamman a kamfanin shirya fina-finan Amurka wato Hollywood inda jarumai mata ke tona asirin yadda diraktoci ke cin mutuncinsu.
Wannan abu ya fara shafan babban dirakta Harvey Weinsten, wanda ya ci mutuncin wasu jarumai don saka su a shirin Fim. Wannan tonon sililin da akewa take da ‘Me too’ ya fara yar yan siyasa da alkali kotun kasar Amurka.
Shin da yan matan Kannywood zasu tona asirin diraktoci masu lalata da me zai faru, Rahama Sadau dai ta ce ‘Tabdijam’
Tauraruwar fina-finan Hausa, Rahama Sadau ta yi fatan cewa zata so ace suma a masana’antar fina-finan Hausa su kwaikwayi irin wancan tsari.
Arewa News 24 ta bada rahoton cewa Rahama ta jinjina maganar, watau inda da za’a yi hakan ‘ Tabdijam’, wanda muka fassara a cewa lallai da asirin mutane da dama ya tonu.
Masu sharhi kan al’amuran yau da kullum sun bayyana cewa wannan baa bun mamaki bane saboda irin gurbacewan tarbiyyan da ke cikin masana’antar fina-finan Hausa.
No comments:
Post a Comment