Hanyar sa komawa Abuja ranar Asabar 25 ga watan agusta shugaba ya nuna gamsuwar sa bisa aikin da sojoji keyi a yankin Zamfara (Instagram/buharisallau)
Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi ma sojoji horo ya bukaci su da kada su sassauta ma yan ta'adda da barayi masu satar mutane da suka addabi yankin Zamfara.
Sojojin jna daga cikin dakarun operation sharan daji da diran mikiya wadanda aka aika jihar Zamfara domin magance matsalar tsaro da al'ummar jihar ke fuskatanta daga yan fashi da barayi masu satar mutane da shanu.
Shugaban yayi wannan kiran ne yayin da ya gana da sojoji a filin jirgin saman Umaru Musa Yar'adua dake nan jihar Katsina gabanin komawar sa Abuja bayan hutun babban sallah da ya gudanar a mahaifar sa.
Shugaba Buhari ya bukaci sojojin da su fatattaki yan ta' adda da suka addabi al'ummar yankin jihar Zamfara (Instagram/buharisallau)
A jawabin sa yayin da ya gana da sojojin shugaba Buhari yana mai cewa ''Na yi matukar gamsuwa kan yadda jami'an tsaro ke jajircewa kuma ina so kada ku sassauta kan ayyukan da kuke yi."
Ya shaida ma sojojin cewa ya zo ne domin ya jinjina masu bisa rawar da suke takawa wajen tabbatar da tsaro a yankin.
Ganawar shi da sojojin ranar asabar 25 ga watan Agusta shugaban ya bukaci sojojin kada su bar yan ta'adda su sha iska tare da nuna gamsuwar sa ga aikin da suke yi.
Al'ummar jihar Zamfara na fuskantar barazana daga yan ta'adda da masu satan mutane da shanu, aika-aikar da suke aikatawa yayi sanadin rasa rayuka da dama tare da sanya jama'a da dama gudun hijira.
Zaman lafiya ya soma samuwa a garuruwan da ta'adanci yayi yawa bisa shirin tsawaita tsaro da gwamnati ta kirkiro na tura dakaru ta musamman jihar domin samad da zaman lafiya.
No comments:
Post a Comment