Jami’an tsaron Kwastom a garin Fatakwal jihar Rivers da suke aikin sintiri sun kama wata babbar kwantenar daukar kaya shakare da kayan sojoji wanda aka yi safararsu daga kasar China, an kama mutum biyu da suke dauke da haramtattun kayan sojojin Wato jama’a akwai wata dabi’a da akeyi a Kasarnan a duk lokacin da rikici ya tashi musamman wanda yake da nasaba da rikicin addini, sai wasu suje suna saka kayan sojoji da ‘yan sanda su hau mota hilux da bindigogi kana ganinsu zaka dauka jami’an tsaron Kasa ne alhali na bogi ne, sunabi suna dauke mutane gida-gida suna kashesu, an jima ana irin wannan barnan musamman a jihar Filato.
Wannan kayan sojoji da jami’an Kwastom suka kama tabbas yana da nasaba da haka, kunga dai yadda kwanaki Kwastom suka kama harsashin bindiga sama da dubu dari biyu, bai wuce kwana biyu ba suka sake kama wasu bindigogi har da wukaken yaki irin na sojoji, yanzu kuma ga kakin sojoji an kama, kunga an hada jami’in tsaron bogi kenan inda an samu nasarar wucewa da kayan, dama ana cewa an tura wasu matasa Kasar Isra’ila sunje suna karban horo irin na sojoji.
Gaskiy ya kamata hukumomi su tsaurara bincike dole a gano wadanda suke daukar nauyin shigo da irin wadannan kayan ta’addanci a hukuntasu bisa doka.
Allah muna rokonKa Ka cigaba da tona musu asiri Amin.
No comments:
Post a Comment