Post Top Ad

Post Top Ad

Sunday, June 3, 2018

Gwamnatin Borno ta fatattaki karuwai dake Maiduguri

Matakin ya biyo bayan wa'adin da ta fitar kwanan baya mai baiwa masu kwana uku kan su tashi daga matattarar karuwai da mashaya da sauran masu aikata ayyukan fasikanci da alfasha dake nan Galadima.

Gwamnatin jihar Borno wanda Alhaji Kashim Shetima ke jagoranta ta dauki mataki na fatattaki karuwai tare da rusa wasu wuraren badala dake garin Maidugurin.

Matakin ya biyo bayan wa'adin da ta fitar kwanan baya mai baiwa masu kwana uku kan su tashi daga matattarar karuwai da mashaya da sauran masu aikata ayyukan fasikanci da alfasha dake nan Galadima.

Wani kwamiti mai karfa da aka kafa kan lamarin karkashin jagorancin kwamishinan shari'a na jihar, Barista Kaka Shehu Lawan tare da goyon bayan ma'aikatar filaye na jihar, sun baiwa gidajen karuwan da na mashayan ranar 29 ga Mayu zuwa 2 ga watan Yuni da su tattara su bar yankunan ko kuma su fuskanci hukunci mai tsanani.

Za a rushe wuraren ne bisa dalilai na rashin mallakar filayen ba bisa ka'ida ba ko kuma yin gini bisa muhallan da ba su dace ba. Ko kuma yin ginin ba tare da mallakar takardu ba.

Kwamishinan ya kuma kara da cewa babu wani daga kafa ko nuna idon sani a yayin da wa'adin kwanaki ukun suka cika.

No comments:

Post a Comment